Na zaci ba zan sake buga kwallo ba — Shaw

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Luke Shaw ya karye ne a karawar da suka yi da PSV Eindhoven

Dan kwallon Manchester United Luke Shaw, ya ce ya ji tsoron watakila ba zai sake buga tamaula ba, sakamakon karyawar da ya yi a kafarsa.

Dan wasan mai tsaron baya mai shekara 21, ya dawo yin wasa bayan da ya murmure daga karayar da ya yi a gasar cin kofin zakarun Turai a cikin watan Satumba.

Shaw ya ce ya yi murna da ya dawo fagen taka-leda a ranar Asabar, kuma ita ce ranar farin cikin da ba zai taba mantawa da ita ba.

Dan kwallon wanda ya karye a karawa da PSV Eindhoven, ya buga minti 45 din farko a wasan sada zumunta da United ta doke Wigan 2-0.

Labarai masu alaka