An tsananta bincike bayan harin Jamus

'Yan sanda a Munich
Image caption Jami'ai sun ce mutum daya ne ya kai harin

'Yan sanda a birnin Munich na Jamus, sun nemi jama'a da su taimaka musu da bayanan hotuna da muryar da suka nada a lokacin da wani mutum ya bude wuta a birnin.

Mutane tara aka kashe sannan wasu 16 suka samu raunuka, uku daga cikinsu munana, a rukunin shaguna na Olympia.

'Yan sanda sun ce dan bingidar, wanda ya kashe kansa daga baya, ba shi da alaka da kungiyar IS.

Har yanzu ba a san dalilan da suka sa mutumin, wanda Bajamushe dan asalin kasar Iran, ya aikata wannan aika-aika ba.

Harin shi ne irinsa na uku da aka kai kan fararen hula a nahiyar Turai a cikin kwanaki takwas, bayan hare-haren birnin Nice da Wuerzburg.

Shirin ko-ta-kwana

'Yan sanda na cigaba da bincike inda ake sa ran za su bayar da karin haske.

An nemi jama'a da su aika hotunan bidiyon da suka nada na hari zuwa wani shafin intanet na musamman da aka bude.

Jami'an tsaro a Jamus sun dade a cikin shirin ko-ta-kwana tun lokacin da wani yaro ya raunata mutane biyar a wani jirgin kasa ta hanyar amfani da wuka.

Kungiyar IS da ke da'awar kafa daular musulunci ta dauki alhakin harin na jirgin kasa.

Hukumomi sun yi gargadin cewa za a iya sake kai hare-hare a kasar.

Labarai masu alaka