Kolo Toure zai koma Celtic

Kolo Toure Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kolo Toure ya taka rawar gani a Ivory Coast

Dan wasan baya na Ivory Coast Kolo Toure zai koma kungiyar kwallon kafa ta Celtic da ke Scotland.

Dan kwallon mai shekaru 35, ya murza-leda a Liverpool karkashin jagorancin Brendan Rodgers wanda yanzu shi ne ke horas da Celtic.

Idan aka kammala gwajin lafiyarsa ba tare da matsala ba, to zai iya taka-leda a wasan da Celtic za ta fafata da FC Astana na share fagen shiga gasar zakarun Turai.

Toure, wanda ya buga wasanni 26 a Liverpool a kakar da ta gabata, zai zamo dan wasa na biyu da Celtic ta saya bayan zuwan Moussa Dembele.

Dan kwallon ya je Manchester United a fan miliyan 14 a 2009, inda ya lashe gasar Premier a 2012, kafin Rodgers ya saye shi zuwa Liverpool a 2013.

Labarai masu alaka