Babu tabbas kan makomar Andre Ayew

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ayew ne ya fi zura wa Swansea

Kocin Swansea Francesco Guidolin ya ce babu tabbas kan makomar Andre Ayew, kodayake ya ce yana fatan dan wasan zai ci gaba da murza leda a kungiyar.

Ana rade-radin cewa Ayew, mai shekara 26, zai koma Sunderland a watan Janairu idan aka bude kasuwar musayar 'yan wasa, kuma wasu rahotanni na cewa zai koma West Ham ko Chelsea.

Guidolin ya ce , "Andre dan wasa ne na gari wanda ya iya taka leda. Ina sa ran zai ci gaba da zama a nan, kodayake babu tabbacin hakan."

Ya kara da cewa yana jiran shugaban kungiyar Huw Jenkins, wanda shi ke kula da sayen 'yan wasa, ya yi masa magana a kan makomar dan wasan.

Ayew ne dan wasan da ya fi zura kwallo a Swansea, inda ya ci kwallaye 12 a kakar wasan da ta wuce bayan ya koma kungiyar daga Marseille a watan Yunin shekarar 2015 a matsayin aro.

Labarai masu alaka