Dogo Mai Takwasara ya buge Shamsu

Image caption Mai Takwasara ya buge Shamsu a turmi na biyu

An ci gaba da wasannin damben gargajiya da yammacin Lahadi a filin wasa na Ado Bayero Square da ke Kano.

Bayan da matasan 'yan dambe suka barje guminsu a filin, nan da nan kuma manyan 'yan wasa suka fara gumurzu a tsakaninsu.

An kara tsakanin Shagon Master Ali daga Arewa da Autan Taye daga Kudu tsawon turmi uku babu kisa.

Haka ma wasan Shagon Sawun Kura daga Arewa da Shagon Bahagon Bala daga Kudu babu wanda ya je kasa.

Shi kuwa Dogo Mai Takwasara Guramada buge Shamsu Kanin Emi na Arewa ya yi a turmi na biyu.

Nura Shagon Dogon Sani daga Arewa a turmin farko ya doke Shamsun Guramada.

Za a ci gaba da dambatawa a ranar Litinin da yammaci a gidan dambem Mamman Basahar da ake kira Danliti dake jihar Kano a Nigeria.