Shugaban Fifa ya sauka a Nigeria

Hakkin mallakar hoto The NFF Twitter
Image caption Shugaban NFF, Amaju Pinnick da Dakta Muhammad Sunusi Sakatare Janar na NFF ne suka tarbe shi

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, Gianni Infantino, ya sauka a Abuja, babban birnin Najeriya, domin fara ziyarar aiki ta kwana biyu.

A lokacin ziyarar, ana sa ran Infantino zai gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari da kuma shugabannin kungiyar kwallon kafar Afirka.

Infantino, wanda aka zaba a watan Fabrairun da ya wuce, ya samu rakiyar sabuwar Sakatare-Janar ta Fifa, Fatma Samoura.

Shafin Twitter na Hukumar Kwallon kafa ta Najeriya, NFF, ya wallafa hoton bidiyon saukar Mista Infantino a filin saukar jiragen sama na Abuja, inda jami'an hukumar suka yi masa maraba.

Sai a ranar Litinin ne zai gana da Shugaba Buhari.

Wasu masu sharhi na ganin ziyarar za ta iya taimakawa wurin shawo kan rikicin shugabancin da ake fama da shi a hukumar ta NFF.

Labarai masu alaka