Zan gaisa da Mourinho idan mun hadu - Guardiola

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyoyin biyu suna yin wasannin atisaye domin tunkarar gasar Premier ta bana

Kociyan Manchester City, Pep Guardiola, ya ce zai yi hannu da Jose Mourinho, mai horar da Manchester United, idan sun zo yin wasan sada zumunta a Beijin a ranar Litinin.

Wasan sada zumuntar da kungiyoyin biyu za su kara, shi ne karo na biyu da masu horarwar za su sake haduwa tun wadda suka yi a 2013 a fafatawa tsakanin Chelsea da Bayern Munich a wasan UEFA Super Cup.

Manajojin kungiyoyin sun yi watsi da hamayyar da take tsakaninsu, inda Guardiola ya ce zai mika masa hannu su gaisa ta mutuntaka.

Mourinho kuwa cewa ya yi, sun yi aiki tare shekara uku a Barcelona, sun kuma horar da manyan kungiyoyi, saboda haka kwararru ne su, kuma dangantakarsu na nan yadda take.

A ranar 13 ga watan Agusta ne za a fara gasar Premier ta Ingila.