Ingila ta yi kyakkyawan zabi — Rooney

Image caption Wayne Rooney ya ce za su ci gaba da yin nasara

Kyaftin din Ingila Wayne Rooney ya ce hukumar kwallon kafar kasar FA ta yi "zabi na gari" da ta nada Sam Allardyce a matsayin sabon kocin kungiyar kwallon kafar kasar.

Allardyce, mai shekara 61, ya sanya hannu a kwantaragin shekara biyu da kungiyar kwallon kafar kasar bayan FA ta amince ta biya Sunderland diyyar barin ta da Allardyce ya yi.

Dan wasan gaba na Manchester United Rooney, wanda kuma shi ne dan wasan da ya fi zura wa Ingila kwallo, na cikin 'yan wasan da suka wakilci kasar a gasar cin kofin Turai da aka yi a Faransa a watan Yuni wadda Iceland ta fitar da su.

Rooney ya ce, "Allardyce zai kawo sauye-sauye a kan yadda 'yan wasan Ingila ke taka leda. Hakan zai yi kyau, kuma watakila zai sa mu yi nasara."

Labarai masu alaka