Mikel Obi zai buga wa Nigeria Olympic

Image caption Siasia ne ke jan ragamar tawagar Nigeria da za ta buga gasar Olympic din

Kyaftin din tawagar kwallon kafar Nigeria, Mikel Obi, yana cikin 'yan wasa 18 da za su wakilci kasar a gasar Olympic da za a yi a Brazil.

Obi mai shekara 28, daya ne daga cikin 'yan wasa uku da suka haura ka'ida, wadanda hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta amince su buga wa tawagar kasa a Olympic.

Sai dai kuma Odion Ighalo na Watford da Kelechi Iheanacho na Manchester City da dan kwallon Arsenal Alex Iwobo, ba za su buga wasannin ba, sakamakon kasa samun izini daga kungiyoyinsu.

Za a fara buga wasannin kwallon kafa kwana biyu kafin ayi bukin bude gasar ta Olympic a ranar 5 ga watan Agusta, wadda Brazil za ta karbi bakunci.

Nigeria wadda ta taba lashe lambar zinare a gasar 1996, tana rukuni na biyu a gasar bana da ya kunshi Sweden da Colombia da kuma Japan.

Masu tsaron raga: Daniel Akpeyi (Chippa FC, South Africa), Emmanuel Daniel (Enugu Rangers)

Masu tsaron baya: Kingsley Madu (AS Trencin, Slovakia), William Troost-Ekong (Haugesund FC, Norway), Ndifreke Udo (Abia Warriors), Saturday Erimuya (Kayseri Erciyespor, Turkey), Abdullahi Shehu (CF Uniao, Portugal), Muenfuh Sincere (Rhapsody FC), Stanley Amuzie (Olhanense FC, Portugal)

Masu wasan tsakiya: John Mikel Obi (Chelsea, England), Okechukwu Azubuike (Yeni Malatyaspor, Turkey), Usman Muhammed (CF Uniao, Portugal), Oghenekaro Etebo (CD Feirense FC, Portugal), Sodiq Saliu (Seraing FC, Belgium)

Masu cin kwallaye: Aminu Umar (Osmalispor, Turkey), Imoh Ezekiel (Al Arabi, Qatar), Sadiq Umar (AS Roma, Italy), Junior Ajayi (CS Sfaxien, Tunisia)

Labarai masu alaka