An dakatar da Niersbach shekara daya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsohon shugaban ya musanta aikata ba dai-dai ba

An dakatar da tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Jamus, Wolfgang Niersbach, daga shiga sabgogin tamaula zuwa shekara daya.

Kwamitin da'ar ma'aikata ne na hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ya samu Niersbach da laifin kin bayyana rahoton aikata ba dai-dai ba kan bayar da cin hanci a neman gurbin karbar gasar kofin duniya ta 2006.

Jamus ce ta samu nasarar lashe zaben da aka yi a cikin watan Yulin 2000, inda ta doke Afirka ta Kudu da 12 da 11.

A watan Nuwambar bara ne Niersbach ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban hukumar kwallon kafar Jamus.

Labarai masu alaka