Juventus ta dauki Higuain daga Napoli

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Higuain tsohon dan kwallon Real Madrid ne

Juventus ta dauki dan kwallon tawagar Argentina, Gonzalo Higuain daga Napoli, kan kudi fam miliyan 75 da 300,000.

Napoli ta ce ta sayar da Higuain mai shekara 28 ga Juventus, wadda za ta biya kudin dan kwallon sau biyu.

Hakan ya sa dan wasan ya zama dan kwallo mafi tsada da aka saya a Italiya, kuma na uku a dan karen tsada a duniya a fagen tamaula.

Higuain ya koma Napoli da murza-leda daga Real Madrid kan kudi sama da fam miliyan 34 a shekarar 2013.

Zuwan Higuain Juventus zai bai wa Manchester United damar daukar Paul Pogba mai shekara 23.

Labarai masu alaka