Cresswell na West Ham United zai yi jinya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar 13 ga watan Agusta za a fara gasar cin kofin Premier

Mai tsaron bayan West Ham United, Aaron Cresswell, zai yi jinyar makonni hudu, kan raunin da ya yi a gwiwar kafarsa.

Cresswell mai shekara 26, ya yi rauni ne a karawar da West Ham ta doke Karlruher ta Jamus a wasan sada zumunta da suka yi a ranar Asabar.

West Ham ta ce dan kwallon zai gana da kwararren likiti, domin tantance idan sai an yi masa aiki a kafar ko kuma akasin hakan.

Cresswell ya koma West Ham da taka-leda daga Ipswich a shekarar 2014.

Labarai masu alaka