'Arsenal ba za ta wuce gona da iri ba'

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Arsenal ba ta dauki kofin Premier ba tun shekarar 2004

Mutumin da ya mallaki Arsenal, Ivan Gazidis, ya ce kungiyar ba za ta kashe makudan kudi domin sayen 'yan wasa kamar yadda abokan hamayyarsu ke yi ba.

Kungiyar dai ta kashe tsabar kudi £35m wajen sayen dan wasa Granit Xhaka daga Borussia Monchengladbachr.

Sai dai Gazidis ya shaida wa jaridar New York Times cewa, "Ba za mu kashe makudan kudi wajen sayen 'yan wasa kamar yadda manyan abokan hamayyarmu suke yi ba. Dole mu rika yin takatsantsan."

Gazidis, mai shekara 51, ya jaddada goyon bayansa ga Arsene Wenger.

Sau 20 a jere Arsenal tana kammala gasar Premier a mataki tsakanin na daya zuwa na hudu a karkashin jagorancin Wenger.

Sai dai rabonsu da su da lashe gasar tun shekarar 2004, abin da ya sa wasu magoya bayan kungiyar suka yi bore a karshen kakar wasan da ta gabata, suna masu yin kira a kore shi.

Labarai masu alaka