Aubameyang zai ci gaba da zama a Dortmund

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Dortmund da Manchester City sun kara a wasan sada zumunta a bana

Borussia Dortmund ta ce tana da tabbacin cewar Pierre-Emerick Aubameyang, zai ci gaba da murza-leda a kungiyar.

Aubameyang wanda yarjejenirsa da Dortmund za ta kare a shekarar 2020, ana alakanta cewar zai koma Manchester City da taka-leda.

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Gabon mai shekara 25, ya ci wa Dortmund kwallaye 25 a kakar wasannin da aka kammala.

Aubameyang ya fada a wata kafar yada labarai ta Jamus cewar ba zai koma wata kungiya ba face Real Madrid.

Labarai masu alaka