Lazio ta dauki Ciro Immobile

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Immobile ya buga wa Italiya wasan gasar cin kofin nahiyar Turai da aka yi a Faransa

Lazio ta dauki dan wasa mai zura kwallo a raga, Ciro Immabile, daga Sevilla, kan kudi da aka ce zai kai fan miliyan bakwai da dubu dari daya.

Immobile ya je Sevilla aro daga Borussia Dortmund a Yulin 2015, daga baya ta saye shi kan kudi Yuro miliyan 11.

Daga nan ne ta bayar da shi aro ga Torino, inda ya ci kwallaye biyar a wasanni 14 da ya buga a gasar wasannin da aka kammala.

Immobile ya buga wa tawagar Italiya wasanni biyu a gasar cin kofin zakarun Turai da aka kammala a Faransa, wadda Portugal ta lashe a karon farko a tarihin tamaular kasar.

Labarai masu alaka