Man City ta daina sa 'yan ƙwallo masu muguwar ƙiba a wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester City za ta yi wasan sada zumunta

Sabon kocin Manchester City Pep Guardiola ya haramta wa 'yan wasan da ke da muguwar kiba da wadanda ke cin abincin da ke sa kiba zuwa wajen atisaye.

Dan wasan baya Gael Clichy ya ce Guardiola ya shaida wa 'yan wasansa su daina cin pizza da wani rukuni na lemon kwalba da abincin da ke sanya kiba.

City ta bude sansanin horas da 'yan wasan da za su buga gasar Premier da Sunderland ranar 13 ga watan Agusta.

Clichy ya ce, "Wannan ne karon farko da wani koci ya taba gaya mana irin haka. Kuma akwai 'yan wasan kungiyar da dama da ba su zo atisaye ba. Idan dan wasa yana da kiba sosai ba zai yi atisaye da mu ba. Ya kamata dan wasan ya sani cewa idan nauyinsa ya wuce kilo 60 zuwa 70, ba zai murza leda da mu ba."

A cewarsa, wasu 'yan wasan na ganin babu komai idan suka yi kiba sosai, amma a zahiri ba haka ba ne.

City za ta fafata da Borussia Dortmund a wasan sada zumunta a birnin Shenzhen na kasar China ranar Alhamis.

Labarai masu alaka