Manchester City za ta dauki John Stone

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kungiyoyi da dama sun yi zawarcin John Stone

Manchester City tana tattaunawa da Everton kan batun sayen dan kwallon tawagar Ingila, John Stone.

Har yanzu ba su kai ga cimma matsaya ba, amma kungiyoyin biyu da suke buga gasar na daf da kulla yarjejeniya.

Watakila City ta sayi Stone kan kudi fam miliyan 50, dan wasan da a bara Chelsea ta yi nacin son daukarsa.

Stone yana cikin tawagar kwallon kafar Ingila da ya wakilce ta a gasar nahiyar Turai, amma bai buga mata wasa ba, inda Iceland ta fitar da ita a wasannin zagaye na biyu.

Labarai masu alaka