Teba ta hana Nasri yin atisaye a Man City

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A cikin watan Agusta za a fara gasar Premier ta bana

Har yanzu Samir Nasri bai buga wa Manchester City, wasannin atisaye da kungiyar ke yi ba, sakamakon kiba da ya kara yi in ji Pep Guardiola.

Nasri mai shekara 29, ya zauna a kan benci a karawar da City ta ci Borussia Dortmund a fafatawar da suka yi a China.

A ranar Laraba mai tsaron bayan City, Gael Clichy, ya bayyana cewar Guardiola ya kori wasu 'yan wasa daga filin atisaye, sakamakon teba da suka kara.

Nasri dan wasan tawagar Faransa ya yi jinyar watanni shida a bara, sakamakon raunin da ya yi a wajen atisayen kungiyar.

Labarai masu alaka