Swansea na sha'awar daukar Llorente

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Za a fara gasar Premier a ranar 13 ga watan Agusta

Kungiyar Swansea City, na sha'awar daukar dan kwallon Sevilla, mai buga wa tawagar Spaniya tamaula Fernando Llorente.

Llorente mai shekara 31, wanda ya ci wa kasarsa kwallaye bakwai a wasanni 24 da ya yi, ana alakanta shi da cewar zai koma Real Sociedad ne da taka-leda.

Haka kuma dan wasan ya zura kwallaye bakwai a karawa 36 da ya buga wa Sevilla a gasar La Liga da aka kammala.

Swansea wadda za ta bayar da Bafetimbi Gomis aro ga Marseille ta kuma tambayi Leicester City, idan za a siyar mata da Leonardo Ulloa.

Labarai masu alaka