U-17 Mata: Nigeria ta gayyaci 'yan wasa 30

Image caption Nigeria za ta wakilci Afirka a gasar cin kofin duniya ta matasa da za a yi a Jordan a bana

Kocin tawagar matasa ta mata ta Najeriya Bala Nikyu, ya gayyaci 'yan wasa 30, domin atisayen karshe na shiga gasar cin kofin duniya ta matasa ta duniya da za a yi a Jordan a bana.

An umarci dukkan 'yan wasan da aka bai wa goron gayyata da su halarci wata ganawa da za a yi a Abuja a ranar Lahadi 31 ga watan Yuli.

An kuma bukaci da su je tare da kayayyakin atisaye, da takardun shekarun haihuwa da sauran takardu da kuma fasfo dinsu.

Najeriya ta kai wannan matakin ne, bayan da ta doke Saliyo da Namibia da Afirka ta Kudu, dukkanninsu gida da waje a fafatawar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta matasa mata da suka yi.

Nigeria wadda ta taba kai wa wasannin daf da na kusa da karshe a gasar shekarar 2010 da 2012 da kuma 2014, tana rukuni daya da Korea da Brazil da Ingila a gasar cin kofin duniya ta shekarar nan.

Labarai masu alaka