Union Bank ya bai wa tawagar Nigeria milyan 30

Hakkin mallakar hoto Union Bank
Image caption Za a yi bikin bude gasar Olympic a ranar 5 ga watan Agusta

Kwamitin wasan Olympic na Nigeria, ya bayyana Union Bank, a matsayin wanda zai tallafawa 'yan wasan tawagar kasar a gasar Olympic da za a yi a Brazil.

Kwamitin ya sanar da hakan ne a ranar Laraba, inda ya ce Union Bank zai bayar da Naira miliyan 30, domin 'yan wasan na Najeriya su taka rawar gani a gasar ta bana.

Tawagar ta Najeriya tana daga cikin kasashen da za su shiga wasannin Olympic da za a fara daga ranar 5 zuwa 21 ga watan Agustan 2016.

Najeriya za kuma ta fafata a wasannin tsalle-tsalle da guje-guje da kokawar zamani da kwallon kafa da kwallon kwando da kuma tennis.

Daraktan Union Bank, Joe Mbulu, ya ce bankin ya dade yana tallafawa 'yan wasan Nigeria fiye da shekara 30 da suka wuce, saboda haka zai ci gaba da marawa Najeriya baya, da nufin zakulo matasan 'yan wasa tun daga tushe.

Union Bank zai tallafawa tawagar Nigeria da za su fafata a wasannin Olympic da kuma wadanda za su kara a wasannin nakasassu da kudi naira miliyan 25, da kuma bai wa kwamitin na Nigeria naira miliyan biyar, domin gudanar da ayyukansa.

Labarai masu alaka