Mourinho ya cancanci zama manaja — Rooney

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sabon kocin Manchester United, Jose Mourinho

Kyaftin din Manchester United, Wayne Rooney ya ce yanzu ya fahimci dalilin da ya sa Jose Mourinho ya yi nasara a harkokin wasanninsa. Ya kuma bayyana sabon kocin kungiyar da wanda ya san abin da yake yi a harkar wasa. A watan Yulin nan ne dai Mourinho ya karbi ragamar jagorancin kulob din na Manchester. Sai dai kuma yayin da Rooney yake yabon kocin nasa, ana tunanin cewa dan wasan kulob din dan kasar Jamus, Bastian Schweinsteiger, na daga ciki 'yan wasa guda tara da za su bar Man Utd.

Labarai masu alaka