Sakamakon damben gargajiya na Abuja

Image caption Wannan takawar babu kisa tsakanin Audu Dan Crespo da Balan Kudawa

Wasanni 10 aka dambata a ranar Lahadi da safe a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

A wasan farko Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa ya buge Bahagon Dogon Minista daga Kudu a turmin farko.

Sauran wasanni takwas da aka dambata canjaras aka yi, sai dai kuma fafatawar da aka rufe fili, Shagon Shagon Autan Faya daga Kudu ne ya buge Shagon Shagon Shamsu daga Arewa.

Ga jerin wasannin da aka yi canjaras babu kisa:

Garkuwan Shagon Mada daga Kudu da Garkuwan Sojan Kyallu daga Arewa

Shagon Shagon Shamsu daga Arewa da Matawallen Kwarkwada daga Kudu

Ginshikin Isa Kasa daga Kudu da Bahagon Abban Na Bacirawa daga Arewa

Bahagon Alin Tarara daga Arewa da Dogon Minista daga Kudu

Shagon Fijot daga Arewa da Shagon Bahagon Sisco daga Kudu

Shagon Shukurana daga Arewa da Shagon Autan Faya daga Kudu

Shagon Bahagon Sisco daga Kudu da Shagon Buzu daga Arewa

Audu Dan Cresfo daga Arewa da Balan Kudawa daga Kudu

Labarai masu alaka