An bayyana 'yan wasan Firimiya da za su Spaniya

Image caption Gasar Firimiyar Nigeria ta hada gwiwa da ta La Liga

Kociyan tawagar kwallon kafa ta Nigeria, Salisu Yusuf, ya bayyana sunayen 'yan wasan da za su je Spaniya domin buga wasanni da wasu kungiyoyin da ke buga La Liga.

'Yan wasan na gasar Firmiyar Nigeria za su kara da Valencia da kuma Malaga daga tsakanin 11 zuwa 13 ga watan Agusta.

Hakan ya biyo bayan hadin gwiwa da hukumar gasar Firimiyar Nigeria ta kulla da ta gasar La Ligar Spaniya domin yin aiki tare.

An umarci 'yan kwallon da aka bayyana sunayensu da su halarci filin atisayen ranar 1 ga watan Agusta, bayan da 8 ga watan Agustan za su tashi zuwa Spaniya.

Ga jerin 'yan wasan da aka gayyata.

Masu tsaron raga: Theophilus Afelokhai Enyimba, Ikechukwu Ezenwa FC Ifeanyiaubah, Emeka Nwabulu Wikki Tourist.

Masu tsaron baya: Etim Matthew Rangers, Ifeanyi Nweke Nasarawa, Chima Akas Enyimba, Gabriel Wassa Tornadoes, Jamiu Alimi Pillars, Emmanuel Ariwachukwu Akwa.

Masu wasan tsakiya: Ifeanyi Ifeanyi MFM, Obinna Nwobodo Rangers, Ekundayo Ojo Sunshine, Rabiu Ali Pillars, Abdullahi Ibrahim Alhassan Wikki, Chales Henlong Wikki,

Masu cin kwallaye: Ezekiel Bassey Enyimba, Joseph Osadiaye Enyimba, Hussaini Mohammed Bata Elkanemi, Chisom Egbuchulam Rangers, Isma'ila Gata Ifeanyiubah, Sakiru Olatunbosun MFM.

Masu jiran kar-ta-kwana: Oluwadamilare Ojo Enyimba, Chinedu Udoji Enyimba.

Labarai masu alaka