Ifeanyiubah ta ci Kano Pillars 2-1

Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Web Site
Image caption An kammala wasannin mako na 29 a gasar Firimiyar Nigeria

Ifeanyiubah ta samu nasara a kan Kano Pillars da ci 2-1 a gasar Firimiya wasan mako na 29 da suka kara a ranar Lahadi.

Ifeanyiubah ce ta fara cin Pillars ta hannun Isma'ila Gata da ka a minti na 30 da fara tamaula.

Bayan da aka dawo ne Pillars ta farke ta hannun Gambo Mohammed, sai dai kuma Ifeanyiubah ta ci ta biyu a bugun fenariti ta hannun Tamen Medrano.

Wasu sakamakon wasannin da aka yi, Enyimba da Rangers tashi suka yi kunnen doki 1-1, Akwa United kuwa uku da babu ko daya ta ci Wikki Tourist.

Ga sakamakon wasannin mako na 29 da aka yi:

  • Shooting Stars 2-1 Sunshine Stars
  • Ifeanyiubah 2-1 Pillars
  • MFM 0-1 Plateau Utd
  • Lobi 3-0 Wolves
  • Akwa Utd 3-0 Wikki
  • Tornadoes 2-1 Abia Warriors
  • Enyimba 1-1 Rangers
  • Nasarawa Utd 3-0 El-Kanemi

Labarai masu alaka