Man City na daf da daukar Sane

Image caption Sane ya fara buga wa tawagar Jamus tamaula a cikin watan Nuwamba

Manchester City ta kusa kammala sayen Leroy Sane daga kungiyar Schalke kan kudi sama da fan miliyan 37.

Schalke ta sanar a ranar Litinin cewar Sane ya ziyarci birnin Manchester, dalilin da ya sa bai bi ta wasannin atisayen da take yi a Austria ba.

A ranar 21 ga watan Yuli ne kociyan Manchester City, Pep Guardiola, ya tabbatar da cewar yana zawarcin Sane.

Jaridun Jamus sun ruwaito cewar dan kwallon tawagar Jamus din ya bukacin izinin barin Schalke a kakar bana, domin ya gwada sa'arsa.

Labarai masu alaka