Man United za ta koma kan ganiyarta - Rooney

Image caption United tana yin atisayen tunkarar wasannin kakar bana

Wayne Rooney ya ce Manchester United za ta koma kan ganiyarta a karkashin sabon koci Jose Mourinho.

Mourinho ya dauki mai tsaron baya Erik Bailly da mai cin kwallaye Zlatan Ibrahimovic da mai wasan tsakiya Henrikh Mkhitaryan domin karfafa wasan United a bana.

A hirar da ya yi da jaridar Daily Mail, Rooney ya ce sabbin 'yan wasan da United ta dauko a bana, za su taimakawa matasan 'yan wasanta Anthony Martial da Marcus Rashford samun karin gogewa a wasanninsu.

Rooney ya yaba da kwarewar da Ibrahimovic ke da ita, ya kuma ce United za ta gagari kungiyoyi idan Paul Pogba ya koma Old Trafford da murza-leda.

Labarai masu alaka