Novak Djokovic ya lashe gasar Toronto

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Djokovic zai buga gasar kwallon tennis a wasannin Olympic

Zakaran gasar kwallon tennis na duniya, Novak Djokovic, ya lashe gasar Roger Cup ta Toronto ta bana.

Djokovic ya doke Kei Nishikori da ci da ci 6-3 7-5 a karawar da suka yi a ranar Lahadi.

Djokovic, mai shekara 29, wanda ya lashe kofuna bakwai a bana, ya samu nasarar doke Nishikori sau tara kenan.

Za a fara gasar Olympic a ranar 5 ga watan Agusta, kuma Djokovic zai wakilci Serbia a gasar kwallon tennis da za a yi a birnin Rio na Brazil.

Labarai masu alaka