Sigurdsson ya sabunta zamansa a Swansea

Hakkin mallakar hoto HUW Evans Picture Agency
Image caption Swansea na fatan Andrew Ayew zai ci gaba da buga tamaula a kungiyar

Dan kwallon tawagar Iceland, Gylfi Sigurdsson, ya saka hannu kan ci gaba da buga wa Swansea tamaula zuwa shekara hudu.

Sigurdsson mai shekara 26, an yi ta rade-radin cewar zai koma Everton da murza-leda kan kudi fan miliyan 25 a kakar wasan bana.

Zaman Sigurdsson a Swansea zai karfafa gwiwar kungiyar, bayan da koci Francesco Guidolin ya sayar da 'yan wasa uku, kuma watakila Ashley William ya koma Everton da taka-leda.

Sigurdsson ya koma Swansea daga Tottenham a watan Yulin 2014.

Labarai masu alaka