Wales ta ki bai wa Hull City koci Coleman

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wales ta taka rawar gani a gasar cin kofin nahiyar da aka yi a Faransa

Hukumar kwallon kafa ta Wales ta ki amincewa da kungiyar Hull City ta tattauna da Chris Coleman kan daukar shi aiki.

Coleman, mai shekara 46, shi ne ya jagoranci Wales a gasar cin kofin nahiyar Turai da aka yi a Faransa a watan Yuli, kuma tuni ya tsawaita zamansa zuwa shekara biyu.

Wales ta ce ta mayar da hankalin ne kan tunkarar wasannin neman gurbin a gasar cin kofin duniya da za a yi a 2018, kuma Coleman zai kai su gaci.

Kociyan Hull City, Steve Bruce, ya ajiye aikin a cikin watan Yuli, bayan da dangantaka ta yi tsami, tsakaninsa da mataimakin shugaban kungiyar Ehab Allam.

Ana rade-radin cewar Roberto Martinez, wanda Everton ta kora a cikin watan Mayu, da kuma tsohon kociyan Amurka, Bob Bradley, suna cikin wadanda Hull za ta tuntuba.

Labarai masu alaka