Ifeanyi na Pillars ya koma Lillstrom ta Norway

Image caption Abba Mouktar mai cinikin 'yan wasan tamaula mai lasisi da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa

Ifeanyi Mathew zai taka rawar gani a gasar kwallon kafa ta Norway in ji wakilin dan wasan Abba Adam Mouktar.

A makon da ya gabata ne Mathew ya saka hannu kan yarjejeniyar buga wa Lillstrom SK tamaula tsawon shekara hudu.

Abba Mouktar ya ce dan wasan yana da kwazo da hazaka, kuma dan kwallo ne mai fahimtar dukkan abinda koci ya bukace shi ya yi.

Ifeanyi dan wasan Kano Pillars ya yi wa El-Kanemi da tawagar matasa ta Nigeria 'yan kasa da shekara 17 da ta 20 wasanni.

Dan kwallon wanda ke buga wa tawagar Super Eagles ta 'yan wasan cikin gida, yana daga cikin masu buga gasar Firimiyar kasar da za su buga da na La Liga a mako mai zuwa.

Labarai masu alaka