Leicester City ta dauki Bartosz Kapustka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Leicester City ta dauki 'yan wasa biyar, domin tunkarar wasannin bana

Mai rike da kofin Premier Leicester City, ta dauki Bartosz Kapustka, daga Cracovia, amma ba zai koma can ba har sai ya samu izinin buga tamaula a Ingila.

Kapustka mai shekara 19, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar kan kudi fan miliyan bakwai da dubu dari biyar.

Dan kwallon ya buga wa tawagar Poland wasanni hudu daga guda biyar da kasar ta yi a gasar cin kofin nahiyar Turai da aka yi a Faransa, wadda Portugal ta lashe.

Kapustka shi ne dan wasa na biyar da kociyan Leicester, Claudio Ranieri ya saya a bana, da suka hada da mai tsaron raga Ron-Robert Zieler da mai tsaron baya Luis Hernandez da mai wasan tsakiya Nampalys Mendy da kuma mai cin kwallaye Ahmed Musa.

Labarai masu alaka