Man City ta dauki Gabriel Jesus daga Palmeira

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jesus zai ci gaba da taka-leda a Palmeiras har zuwa watan Disamba

Manchester City ta dauki matashin dan wasa mai shekara 19, dan kasar Brazil, mai suna Gabriel Jesus daga Palmeiras kan kudi fan miliyan 17.

Jesus ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar, amma zai ci gaba da murza-leda a Palmeiras har zuwa karshen kakar gasar Brazil, wadda za ta kare a watan Disamba.

Dan wasan ya ci wa Palmeiras kwallaye 26 a wasanni 67 da ya yi, kuma shi ne ke kan gaba a yawan cin kwallaye a gasar ta Brazil.

Guardiola sabon kociyan City ya kashe fan miliyan 100 wajen sayo sabbin 'yan wasa a bana da suka hada da Ilkay Gundogan da Nolito da Oleksandr Zinchenko da kuma Aaron Mooy.

Labarai masu alaka