Olympic:Tawagar Nigeria ta samu jinkirin isa Rio

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption NFF ta ce canja kudin jirgin daga naira zuwa dala ne ya janyo jinkirin biyan

Tawagar 'yan kwallon Najeriya da za su yi wasa a gasar Olympic ta samu jinkirin zuwa birnin Rio saboda jirgin da zai kai su ya bukaci a biya shi kudinsa baki daya.

Tun a makon jiya ne dai ya kamata tawagar ta bar birnin Atlanta, inda 'yan wasan suka yi horo a Amurka, sai dai har zuwa ranar Talata basu tashi zuwa Brazil ba.

Wata majiya da ke da kusanci da hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta ce an samu 'yar matsala ce ga me biyan kudin jirgin da zai kwashe 'yan wasan zuwa Rio.

Majiyar ta shaida wa BBC cewa kowa 'kowa a hukumar kwallon ya damu' ganin cewa karawar da Najeriyar za ta yi na farko da ƙasar Japan za a yi shi ne a ranar Alhamis mai zuwa.

Daya daga cikin 'yan wasan ya gaya wa BBC cewa "An ce mana mu shirya za mu tafi nan da 'yan sa'oi, amma tun makon jiya haka zancen yake."

Daga baya an samu tabbacin cewar tawagar ta Nigeria za ta isa birnin Rio na Brazil a ranar Laraba domin shiga wasan kwallon kafa ta maza.

A gasar ta Rio dai Nigeria na cikin rukunin 'B' tare da Sweden da Colombia da kuma Japan, kuma Najeriyar ta bugi ƙirjin kafa tarihi a gasar.