Olympic: Nigeria za ta bar Amurka a ranar Laraba

Hakkin mallakar hoto TheNFF twitter
Image caption Nigeria za ta kara da Japan a gasar kwallon kafa ta maza a ranar Alhamis

An bayar da tabbacin cewa tawagar matasan Nigeria 'yan kasa da shekara 23 za su bar Amurka a ranar Laraba, domin isa birnin Rio na Brazil.

Nigeria za ta kara da Japan a wasan rukuni na biyu da za su yi gumurzu a ranar Alhamis a filin wasa na Manaus.

Tawagar ta Nigeria ta samu jinkirin isa Brazil, bayan da jirgin da aka dauka haya ya ki dibar 'yan wasan da masu horas da su kan batun biyansa ladan jigila.

Ministan wasanni na Nigeria, Barrista Solomon Dalung, ya ce ya kara biyan kamfanin jirgin karin wasu kudin.

Wasu daga cikin 'yan wasan sun damu matuka cewar rashin samun hutu isasshe zai iya shafar kwazon wasan da za su kara da Japan.