Llorente ya koma Swansea da taka-leda

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Swansea tana kara karfin kungiyar domin tunkarar wasannin bana

Kungiyar Swansea City, ta cimma yarjejeniyar daukar dan kwallon Sevilla, mai buga wa tawagar Spaniya tamaula Fernando Llorente.

A ranar Juma'a likitocin Swansea, za su duba lafiyar Llorente mai shekara 31, wanda ya ci wa kasarsa kwallaye bakwai a wasanni 24 da ya yi mata.

Haka kuma dan wasan ya zura kwallaye bakwai a karawa 36 da ya buga wa Sevilla a gasar La Liga da aka kammala.

Swansea wadda ke shirin tunkarar gasar Premier ta bana ta kuma tambayi Leicester City, idan za a siyar mata da Leonardo Ulloa.

Labarai masu alaka