Gwarzon Turai: Bale ko Ronaldo ko Griezmann?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar 25 ga watan Agusta za a zabi gwarzon dan kwallon kafa na Turai na bana

An fitar da sunayen 'yan wasa uku wadanda za a zabi wanda ya fi yin fice a fagen tamaula a nahiyar Turai a bana.

'Yan wasa ukun su ne Gareth Bale dan kasar Wales mai wasa a Real Madrid da Cristiano Ronaldo na Portugal da dan wasan Atletico Madrid dan kwallon tawagar Faransa.

Dan kwallon Barcelona, Lionel Messi, wanda ya lashe kyautar sau biyu a jere, ya kare a mataki na biyar kafin a fitar da sunayen uku.

A ranar 25 ga watan Agustan nan ne 'yan jarida daga mambobin kasashen hukumar kwallon kafa ta Turai za su zabi gwarzon dan kwallon kafa na Turai na bana.

Labarai masu alaka