Arsenal ta ci Man City a wasan sada zumunta

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar 13 ga watan Agusta za a fara gasar Premier ta bana

Arsenal ta samu nasara a kan Manchester City da ci 3-2 a wasan sada zumunta, domin shirin tunkarar wasannin bana da suka kara a Gothenburg.

Raheem Sterling ne ya fara cin Arsenal, sai dai kuma Alex Iwobi ya farke, sai Theo Walcott da kuma Chuba Akpom suka kara kwallaye a ragar City.

Daga baya ne dan wasan tawagar Nigeria, Kelechi Iheanacho ya ci wa City kwallo ta biyu a karawar.

Sai dai kuma mai tsaron baya na Arsenal, Gabriel sai fitar da shi aka yi daga filin, sakamakon raunin da ya yi.

A dai wasannin sada zumuntar da aka yi a ranar Lahadi, Chelsea ta doke Werder Bremen da ci 4-2, ita kuwa Liverpool kwallaye hudu da babu ko daya Mainz ta zura mata a raga, kwana daya kacal da ita ma ta ci Barcelona hudu da babu ko dayan.

Southampton kuwa daya mai ban haushi ta ci Athletic Bilbao a karawar da suka yi a filin wasanta na St Mary, kuma Shane Long ne ya ci kwallon.

Labarai masu alaka