Man United ta dauki Community Shield

Image caption Man United ta lashe Community Shield sau 11 kenan jumulla

Manchester United ta lashe Community Shield na bana, bayan da ta doke Leicester City da ci 2-1 a karawar da suka yi a ranar Lahadi a filin wasa na Wembley.

Jesse Lingard ne ya fara ci wa United kwallo tun kafin a je hutun rabin lokaci, bayan da aka dawo ne Leicester City ta farke ta hannun Jamie Vardy.

Saura minti bakwai a tashi daga karawar sabon dan wasan da United ta sayo a bana Zlatan Ibrahimovic, ya ci mata na biyu.

Da wannan nasarar da Manchester United ta samu ya sa ta dauki Community Shield na 11 jumulla, Arsenal tana da shi guda shida sai Chelsea mai guda uku a tarihin gasar.

Ana buga Community Shield ne tsakanin wadda ta lashe kofin Premier da aka kammala da kungiyar da ta dauki kofin kalubale na Ingila a shekarar.

Kuma kammala karawar na nufin mako mai zuwa za a fara gasar Premier ta Ingila.

Labarai masu alaka