Dalung ya nemi afuwar 'yan kwallon Nigeria a Olympic

Hakkin mallakar hoto The NFF Twitter
Image caption Tawagar Nigeria ta kai wasan daf da na kusa da karshe

Ministan wasanni na Nigeria, Barista Solomon Dalung, ya nemi afuwar 'yan wasan tawagar Nigeria 'yan kasa da shekara 23 kan kalubalen da suka fuskanta kafin isarsu Brazil.

'Yan wasan na Nigeria sun kusa makara zuwa birinin Rio domin buga wasan kwallon kafa da Japan a karawar farko ta cikin rukuni, daga baya Nigeria ta samu nasara da ci 5-4.

Tawagar ta Nigeria ta samu jinkirin isa Brazil, bayan da jirgin da aka dauka haya ya ki dibar 'yan wasan da masu horas da su kan batun biyansa ladan jigila.

A cewar mai magana da yawun hukumar kwallon kafa ta Nigeria, Ademola Olajire, ministan ya nemi afuwar 'yan wasan ne, bayan da ya kammala kallon karawar da tawagar ta ci ta Sweden daya mai ban haushi.

Kyaftin din Nigeria, Mikel Obi, ya ce za su yi kokarin da ya kamata domin kasar ta lashe lambar zinare a fagen tamaula.

Nigeria ta taba daukar lambar zinare a wasan Olympic da aka yi a Atlanta a shekarar 1996.

Labarai masu alaka