Lithuaniya ta ci Nigeria a kwallon kwando

Hakkin mallakar hoto Twitter Basketball Nigeria
Image caption Nigeria ta yi rashin nasara a wasanni biyu a jere kenan

Lithuaniya ta samu nasara a kan Nigeria da ci 89 da 80 a wasan kwallon kwando a gasar wasannin Olympic da ake yi a birnin Rio na Brazil.

Nigeria ce ta fara samun nasara da ci 16 da 13 a zangon farko, a kuma zango na biyu ma dai Nigeria ta ci 25 da 23.

Ana kaiwa zango na uku ne Lithuaniya ta ci Nigeria da ci 29 da 13, a karashen wasa aka doke Nigeria da ci 89 da 80.

Nigeria wadda ta yi rashin nasara a wasan farko a hannun Argentina za ta buga wasan gaba a ranar Alhamis da Spaniya.

Labarai masu alaka