Olympic: Tauraruwar ɗan Nigeria ta haska a Tennis

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wannan ne karo na biyu da Aruna ke halartar gasar Olympic

Wani ɗan wasan Nigeria, Aruna Quadri ya isa wasan dab da na kusa da karshe a wasan Tennis na maza da ake yi a gasar Olympic.

Shi ne kuma bakin fata ɗan Afrika na farko da ya taɓa kai wa wannan matakin a gasar ta Olympic.

Aruna dai ya doke wani Bajamushe, Timo Boll wanda ya ɗauki tagulla a gasar Olympic da aka yi a birnin London a shekarar 2012.

A cikin mintuna 16 kacal ɗan Najeriyar ya doke Boll wanda shi ne na 13 a wasan Tennis a duniya, inda ya ci 4-2 a zagaye na hudu.

'Yan ƙasar Brazil dai sun yi ta shewa tare da nuna goyon bayansu ga ɗan wasan Najeriyar mai shekaru 28 a duniya.

Labarai masu alaka