Januzaj yana son barin Manchester United

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Adnan Januzaj, dan wasan gaba na Manchester United.

Dan wasan gaba na Manchester United, Adnan Januzaj yana son ya bar kulob din gabadaya saboda Jose Mourinho bai sa shi a jerin 'yan wasan kungiyar na farko ba.

Kwantaragin dan wasan wanda dan asalin kasar Belgium ne dai za ta kare a 2018 amma kulob din yana son ya tafi a musayar 'yan wasa.

Amma Januzaj ya fi son ya tafi ba ta hanyar musayar 'yan wasa ba.

Ana dai tunanin dan wasan mai shekara 21 yana son zuwa Sunderland ne sannan kuma an ce wasu kungiyoyi a Italiya da Spaniya suna zawarcin sa.

Labarai masu alaka