Nigeria ta yi rashin nasara a hannun Spaniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karo na uku kenan Nigeria ta yi rashin nasara a wasan kwallon kwando a Rio

Tawagar Nigeria ta kwallon kwando ta maza ta yi rashin nasara a hannun ta Spaniya da ci 96 da 87 a wasan Olympic da suka kara.

Spaniya ce ta fara cin wasan zangon farko da ci 25 da 11, yayin da Nigeria ra samu cin zango na biyu da ci 30 da 18 da zango na uku da ci 25 da 22.

A karawar zango na hudu ne Spaniya wadda ita ce ke mataki na biyu a jerin kasashen da suka fi iya kwallon kwando a duniya ta ci Nigeria da ci 21 da 31.

Nigeria wadda ta yi rashin nasara a hannun Argentina da Lithuania za ta fafata da Croatia a ranar Lahadi.

Labarai masu alaka