Murray ya ci lambar zinare a Brazil

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Murray shi ne ke mataki na biyu a jerin wadan da suka fi iya kwallon tennis a duniya

Andy Murray ya zama dan kwallon tennis na farko da ya ci lambar zinare a gasar Olympic biyu a jere.

Murray dan Birtaniya, ya sami nasarar doke Juan Martin del Potro na Argentina da ci 7-5 4-6 6-2 7-5 a karawar da suka yi sama da awa hudu.

Murray mai shekara 29, wanda ya lashe gasar Wimledon mako biyar da suka wuce, shi ne ya lashe zinare a gasar Olympic da aka yi Landan a 2012.

Kei Nishikori na Japan ne ya ci lambar tagulla, bayan da ya doke Rapael Nadal da ci 6-2 6-7 (1-7) 6-3.

Labarai masu alaka