Barcelona ta ci Sevilla a Spanish Super Cup

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barcelona za ta karbi bakuncin Sevilla a ranar Laraba a wasa na biyu

Barcelona ta doke Sevilla da ci 2-0 a wasan farko a Spanish Super Cup da suka kara a ranar Lahadi.

Luis Suarez ne ya fara cin kwallo, sannan Munir El Haddadi ya kara ta biyu a ragar Sevilla.

Kungiyoyin biyu za su kara a wasa na biyu a ranar Laraba a filin wasa Camp Nou.

Hakan kuma na nufin za a fara gasar cin kofin La Liga na Spaniya a ranar Juma'a, inda Barcelona wadda ke rike da kofin za ta karbi bakuncin Real Betis.

Labarai masu alaka