Ancelotti ya dauki kofi a Bayern Munich

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Carlo Ancelotti ne ya maye gurbin Pep Guardiola a Bayern Munich

Carlo Ancelotti ya dauki kofin farko a Bayern Munich, bayan da kungiyar ta doke Borrusia dortmund da ci 2-0 a Super Cup na Jamus.

Arturo Vidal ne ya fara cin kwallo, sannan Thomas Muller ya ci ta biyu, wanda hakan ya ba ta damar lashe kofin farko a kakar wasanni ta bana.

Dortmund ta kai hare-hare masu zafi ta hannun Pierre-Emerick Aubameyang da kuma Ousmane Dembele.

Kammala wannan wasan na nufin fara gasar cin kofin Bundesliga a ranar 26 ga watan Agusta, kuma Munich mai rike da kofin za ta fafata ne da Werder Bremen.

Ancelotti ya maye gurbin Pep Guardiola wanda ya koma horar da Manchester City.

Labarai masu alaka