Sakamakon wasannin damben gargajiya

Image caption Bahagon Gurgun Bala da Alin Tarara, babu kisa a takawar da suka yi

Kimanin wasanni tara aka dambata da safiyar Lahadi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Sai dai kuma wasanni biyu ne aka yi kisa da suka hada da karawar da Abban Na Bacirawa daga Arewa ya buge Autan Faya daga Kudu.

Da kuma wani bakon dan dambe da ya tari Sanin Kwarkwada daga Kudu, kuma a turmin farkon Sanin Kwarkwada ya nuna ruwa ba sa'an kwando bane.

Ga sauran wasannin da aka yi canjaras:
  • Shagon Autan Faya daga Kudu da Shagon Inda daga Arewa
  • Garkuwan Dan Sharif daga Kudu da Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa
  • Shagon Bahagon Musa daga Arewa da Shagon Sadam Nussaini daga Kudu
  • Shagon Lawwalin Gusai daga Arewa da Matawallen Kwarkwada daga Kudu
  • Dan Langa-Langa daga Kudu da Shagon Babangida daga Arewa
  • Bahagon Gurgun Bala daga Kudu da Bahagon Alin Tarara daga Arewa

Labarai masu alaka