Olympic: Nigeria za ta kara da Jamus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria ta taba lashe lambar zinare a wasan kwallon kafa a 1996

Tawagar matasa 'yan kasa da shekara 23 ta Nigeria za ta kara da ta Jamus a wasan daf da na karshe a kwallon kafa ta maza a Brazil.

Nigeria ta kai wannan matakin ne bayan da ta ci Denmarka 2-0 a wasan daf da na kusa da karshe da suka yi a ranar Asabar.

Ita kuwa Jamus za ta fafata ne da Nigeria, bayan da ta samu nasara a kan Portugal da ci 4-0.

Brazil mai karbar bakunci wadda ta doke Colombia da ci 2-0 za ta kece raini ne da Hounduras wadda ta ci Korea ta Kudu daya mai ban haushi.

Za a buga dukkan wasanni biyu na daf da karshe a kwallon kafar maza a ranar Laraba.

Labarai masu alaka