Benteke na son barin Liverpool

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Benteke ya je Liverpool a lokacin tsohon kocin Liverpool, Brendan Rodgers

Kulob din Liverpool ya yi watsi da tayin da Crystal Palace ya yi wa dan wasan kungiyar na gaba, Christian Benteke, na £30m.

Za a dai a bayar da £23m da farko sannan kuma daga bisani a kara £7m.

Benteke, mai shekara 25 ya samu matsala da Jurgen Klopp tun lokacin da ya karbi jagorancin kulob din a watan Octoba.

Christian ya je Liverpool ne a watan Yulin 2015 a lokacin tsohon kocin kulob din Brendan Rodgers, a kan £32.5m.

Dan wasan wanda ya ci wa Liverpool kwallaye 10, ya bayyana aniyarsa ta barin kulob din idan har suka cigaba da 'yar tsama da Jurgen Klopp.

A ranar Litinin ne dai Crystal Palace ta sayar da dan wasanta na gefe, Bolaise Yannick ga Everton, a kan kudi £25m.

Labarai masu alaka